News
Gwamnatin Kano Ta Yabawa Gwamnatin Tarayya Bisa Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar NCC A Jihar
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana godiyarta ga Gwamnatin Tarayya bisa kammala gyaran da ta yi wa cibiyar NCC Digital Industrial Park da ke cikin sakatariyar Audu Bako a Kano, wadda aka lalata a watan Agusta na shekarar 2024 yayin wata zanga-zangar rashin jin daɗin halin tattalin arziki.
Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana haka a ranar Laraba yayin bikin ƙaddamar da sabon ginin cibiyar, ƙarƙashin jagorancin Ministan Sadarwa, Kirkire-Kirkire da Tattalin Arziki, Dakta Bosun Tijjani.
Karamar Hukumar Rogo ta ɗauki sabon salo na ayyukan jin ƙai da ci gaba
Gwarzo ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gamsu matuƙa da yadda Ministan ya cika alƙawarin da ya ɗauka a lokacin ziyarar da ya kai Kano a bara, inda ya sha alwashin dawo da cibiyar cikin aiki cikin ƙanƙanin lokaci.
Ya ce ƙaddamar da cibiyar ba wai kawai alama ce ta kishin kasa ba, har ila yau wata dama ce da za ta farfaɗo da sha’awar fasaha da kere-kere a zukatan matasa, da samar da sabbin hanyoyin ci gaban masana’antu a Kano da ma Arewacin Najeriya gaba ɗaya.
Minista Tijjani: “Na rantse sai na dawo da cibiyar — kuma na cika”
A nasa jawabin, Minista Bosun Tijjani ya ce a lokacin da ya ziyarci cibiyar da aka lalata a bara, ya ɗauki alƙawarin dawo da ita domin matasan Arewacin Najeriya su ci moriyar fasahar zamani.
Ya ce a cikin shirin horar da matasa da ma’aikatar ta kaddamar a baya-bayan nan, mutum miliyan ɗaya da dubu dari takwas ne suka nemi shiga, kuma cikin adadin nan, jihar Kano ce ta fi yawan masu nema da kaso 10 cikin 100 – abin da ya nuna irin jajircewar matasan jihar wajen ɗaukar fasaha da kirkire-kirkire a matsayin makomar rayuwa.
Dakta Tijjani ya kuma mika sakon ta’aziyya ga al’ummar jihar Kano bisa rasuwar Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya bayyana a matsayin gwarzon arziki da zaman lafiya.
A ƙarshen taron, gwamnatin jihar Kano ta karrama Ministan da sarautar Sarkin Yaƙin Ƙirƙire Fasahar Sadarwa, inda aka sanya masa malafa tare da rataya masa takobi – a matsayin girmamawa da yabon kishin ƙasa.
