Connect with us

News

Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Ruftawar Bene Mai Hawa Uku

Published

on

c264abdd 1be1 4265 b524 1048546d4e4b.jpg

Wani gini mai bene uku da ke unguwar Legas Island ya rufta a safiyar Alhamis, lamarin da ya jikkata wasu daga cikin mazauna cikin ginin.

Ginin da ke kan titin Asesi, kusa da titin Adeniji Adele, ya rufta ne ba tare da wani rahoton gargadi ko bayyanannen dalili ba, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici da rudani.

Advertisement

Ƴan Bindiga Sun Farmaki Gidan Tsohon Minista A Filato, Sun Kashe Mace Ɗaya

Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Legas, Gbenga Omotoso, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa an ceto mutane hudu daga cikin baraguzan ginin, kuma tuni an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likita.

 

Advertisement

Jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), tare da haɗin guiwar sauran hukumomin da abin ya shafa, sun isa wurin da ginin ya rufta domin gudanar da ayyukan ceto da kuma tabbatar da lafiyar sauran mutanen da ke kusa da wurin.

A halin da ake ciki, hukumomi na ci gaba da kokarin gano ko akwai sauran mutane da ke karkashin baraguzan ginin, tare da gudanar da bincike kan musabbabin ruftawar.

Advertisement

 

BBC HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending