News
Wasu Matasa Sun Damke Masu Kwacen Waya, Sun Mika Su Hannun ’Yan Sandan A Kano
Wasu matasa biyu da ake zargi da kwacen waya sun shiga hannu a unguwar Bachirawa da ke Kano, bayan da jama’ar yankin suka kama su tare da mika su ga rundunar ’yan sanda.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Yanzu Haka Adadin Hadiman Da Ke Aiki Da Gwamnan Kano Sun Haura Su 300
A cewar Kiyawa, matasan sun tare wata mata ne suka kwace mata wayar hannu, sai dai daga bisani al’umma suka yi kukan kura suka kamo su.
“An cafke su da wata wuka a hannunsu, kuma an samu nasarar kwato wayar da suka kwace wa matar,” in ji SP Kiyawa.
Yanzu haka, matasan na hannun ’yan sanda domin ci gaba da gudanar da bincike.
Rundunar ’yan sandan ta yaba da irin wannan haɗin kan da al’umma ke bayarwa, tana mai cewa irin wannan mataki na ƙara taimakawa wajen rage aikata laifuka a cikin al’umma.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
