News
Ko Tinubu Ya Nada Ɗansa Seyi Tinubu Shugaban INEC, Sai APC Ta Fadi A 2027 – Dalung
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa duk wani yunkuri da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi na nada na kusa da shi a muhimman mukamai, ba zai hana jam’iyyarsa ta APC shan kaye a zaben 2027 ba.
Dalung ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da tashar NEWS CENTRAL, inda ya ce rashin jin dadin da ‘yan Najeriya ke ciki a halin yanzu ya isa ya haifar da sauyin gwamnati a zabe mai zuwa.
“Ko Tinubu ya nada ɗansa Seyi Tinubu shugaban INEC, kuma ya nada matarsa a matsayin Babbar Alkalin Ƙoli, kuma gwamnoni 36 su koma APC, ba zai hana su faduwa ba. Jama’a sun gama gajiya,” in ji shi.
Dalung ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaza, tana zaluntar jama’a, ta kuma mayar da fatara da yunwa da matsin rayuwa tamkar makaman yaki da talakawa.
“Zaben 2027 zai zama tsakanin ‘yan Najeriya da gwamnatin Tinubu. Gwamnatin nan ta bayyana cewa ta shiga yaki da jama’a ta hanyar tsananta rayuwa.”
Ya kara da cewa hanya daya da za a iya kawo karshen wannan tsarin ita ce jam’iyyun adawa su hade a karkashin kawancen sabuwar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin kalubalantar APC a 2027.
“Lokaci ya yi da ‘yan adawa za su cire bambance-bambance su tsaya tsayin daka domin ceto kasar nan daga halin kunci da ake ciki.”
Dalung ya jaddada cewa dole ne ‘yan Najeriya su tashi tsaye, su shirya tsaf domin kada su sake fadawa hannun gwamnati irin ta yanzu da ke kara jefa su cikin kunci.
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News13 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
