Connect with us

News

Trump Ya Yi Barazanar Karin Haraji Ga Kasashen Da Ke Son Kusantar BRICS

Published

on

Trump

Shugaba Trump ya yi kashedin cewa duk kasar da za ta goyi bayan manufofin Kungiyar BRICS na adawa da Amurka za ta fuskanci karin haraji na kashi 10 cikin 100 ba tare da daga kafa ba.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar labta sabon karin harajin kwastom na kashi 10 cikin 100 ga kasashen da za su yi kuskuren kusantar Kungiyar BRICS wadda ta kunshi kasashe 10 da tattalin arzikinsu ke habaka kuma ke wakiltar kusan rabin al’ummar duniya.

Advertisement

Fursunoni 58 Sun Rubuta Jarabawar NECO A Gidan Yarin Kano

A wani sako da ya wallafa a shifinsa na Truth Social a ranar Lahadi, Trump ya yi kashedin cewa duk kasar da za goyi bayan manufofin kungiyar BRICS na adawa da Amurka za ta fuskanci karin haraji na kashi 10 cikin 100 kuma ba za a daga wa ko wacce kasa kafa a game da wannan mataki ba.

Kazalika Trump ya kuma ce a wannan Litinin za a fara aikewa da wasikun farko na barazanar labta harajin kwastam mai tsauri ga kasashen da har yanzu ba su cimma yarjejeniyar kasuwanci da Amurka bisa sabon shirinsa ba.

Advertisement

Kungiyar ta BRICS da ke kammala taronta na shekara-shekara a Brazil a wannan Litinin ta bayyana damuwa a game da barazanar ta Trump, inda ta yi gargadi a game da yadda irin wadannan matakai ke raunana tafiyar tattalin arzikin duniya.

 

Advertisement

 

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending