News
Zazzafar Arangama Tsakanin Magoya Bayan Sarakuna Biyu Ta Janyo Binciken ‘Yan Sanda
Rundunar ‘Yan Sanda a jihar Kano ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da na Sarkin Kano na 15 , Aminu Ado Bayero, a unguwar Kofar Kudu.
Rikicin ya afku ne a ranar da Sarki Aminu Ado Bayero ke wucewa daga Mandawari zuwa fadar Nassarawa, inda wasu daga cikin magoya bayan Sarki Muhammadu Sanusi II suka tare hanyar da tawagar ta ke bi, abin da ya janyo hargitsi da asarar dukiyoyi.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an raunata wasu daga cikin dogaran Sarakunan, an lalata wasu gine-gine ciki har da ƙofa, tare da fasa wata motar ‘yan sanda da ke cikin rakiyar tawagar.
Rundunar ‘yan sanda ta yi gaggawar kawo dauki ta hanyar harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa matasan da ke rikicin, da nufin hana rikicin yin kamari ko rikidewa zuwa rikici na siyasa ko na kabilanci.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kafa kwamitin bincike domin zakulo musabbabin rikicin tare da daukar matakin doka kan wadanda suka aikata laifi.
“Mun kafa kwamitin bincike da zai bankado abubuwan da suka janyo rikicin. Har ila yau, rundunar za ta dauki mataki kan duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan lamari,” in ji SP Abdullahi Haruna.
A halin yanzu dai, rundunar ‘yan sanda na ci gaba da tsaurara matakan tsaro a wasu muhimman wurare da suka hada da fadar Sarakuna domin kare lafiyar jama’a da kuma dakile yaduwar tashin hankali.
