Connect with us

News

Gwamnan Katsina Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Hadarin Mota 

Published

on

Majalisar dokokin Jihar Katsina ta amince da ƙirƙiro gundumomi guda shida a jihar

Rahotanni daga jihar Katsina sun tabbatar da cewa Gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Radda, ya tsira lafiya bayan da wata mota ta yi karo da ayarin motocinsa a kan hanyarsu ta dawowa daga Daura zuwa Birnin Katsina.

Gwamna Radda ya halarci taron gaisuwar rasuwar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari, wanda aka gudanar a garin Daura. Yayin dawowar sa ne lamarin ya faru.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu Ya Kamu Da Ciwon Kumburin Hanji

Wani jami’in gwamnatin jihar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa DCL HAUSA cewa wata mota ta goge daya daga cikin motocin ayarin gwamnan, wanda hakan ya janyo hadarin.

“Gaskiya ne, akwai hadari da ya faru, amma Alhamdulillah, Gwamna Radda yana cikin koshin lafiya. Akwai wani daga cikin jami’anmu da ake zaton ya samu raunuka masu sauki,” in ji jami’in.

Rahoton ya ce hukumomi na ci gaba da bincike game da yadda lamarin ya faru da kuma tabbatar da lafiyar wadanda lamarin ya rutsa da su.

Wannan ba shi ne karon farko da irin wannan hadari ke faruwa da ayarin jami’an gwamnati ba, inda masana tsaro ke kara jan hankalin masu ruwa da tsaki da su kara sa ido da kiyaye dokokin hanya wajen zirga-zirgar manyan jami’an gwamnati.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending