Connect with us

News

EFCC Ta Cafke Daliban BUK 24 Da Ake Zargi Da Damfara Ta Yanar Gizo A Kano

Published

on

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), ta cafke dalibai 24 na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) bisa zargin aikata damfara ta yanar gizo, a wani samame da jami’anta suka kai a unguwannin da ke kusa da harabar jami’ar, ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025.

Rahotanni daga hukumar sun bayyana cewa samamen ya biyo bayan sahihan bayanai da hukumar ta samu dangane da yadda wasu matasa ke amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen aikata zamba da satar bayanan sirri na mutane.

Advertisement

Cutar Amai da Gudawa Ta Yi Ajalin Mutum 12, Ta Kwantar da Fiye Da 230 A Asibiti A Neja

A cewar sanarwar da ofishin EFCC na Kano ya fitar, duka wadanda aka kama dalibai ne a Jami’ar Bayero ta Kano, kuma ana zarginsu da hannu a damfara ta yanar gizo da zamba ta kudi.

Kayan da aka kwato daga hannunsu sun hada da wayoyin salula, kwamfutocin tafi-da-gidanka, na’urorin samun intanet, da mota kirar Honda Accord.

Advertisement

Sunayen wadanda aka kama sun hada da: Ismaíl Nura, Suuleyman Ayeh, Usman Abdulrazaq, Emmanuel Chigozie, Akabe Seth, Daniel Imoter, Abdulganiyu Jimoh, Jafar Abubakar, Usman Nuraddeen, Mohammad Adnan, Abubakar Abusufyan, Abdulmalik Ibrahim, Abubakar Sadiq, Daniel Masamu, Abdulrasheed Abdulsamad, Issac Dosunu, Nuraddeen Ogunbiyi, Onyeyemi Kaleem, Miracle Joseph, Danjuma Musa, Ibrahim Mubaraq, Yusuf Salihu, Lawal Ibrahim Edebo, Abdulmajeed Suleiman da Dauda Abdulhamid.

EFCC ta ce samamen ya biyo bayan dogon bincike da ya tabbatar da alaka tsakanin wadanda ake zargin da aikata laifuka kamar damfara ta yanar gizo, satar bayanan sirri da kuma karkatar da dukiyoyin jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending