Connect with us

News

Gwamnatin Kano Za Ta Haɗa Gwiwa Da NEPC Don Wayar Da Kan Jama’a Kan Fitar Da Kaya Zuwa Ketare

Published

on

1753871255667948 0

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta haɗa gwiwa da hukumar fitar da kaya zuwa ketare (NEPC) domin wayar da kan al’umma kan hanyoyin da za su bi wajen shiga harkar fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a lokacin da Ko’odinetar NEPC na yankin Arewa maso Yamma, Hajiya Amina Abdulmalik, ta kai masa ziyara a ofishinsa da ke Kano.

Gobara Ta Kone Dakin Kwanan Dalibai Mata A  Kano

Kwamared Waiya ya ce akwai gagarumar gibin fahimta tsakanin al’umma da ayyukan NEPC, wanda hakan ke hana mutane da dama cin moriyar shirye-shiryen da hukumar ke gudanarwa.

“Abin takaici ne ganin cewa wasu da ba mazauna Kano ba ne ke zuwa suna rajista domin su amfana da shirin, alhali ‘yan asalin jihar ba su da masaniya,” in ji shi.

Ya ce Ma’aikatar Za ta fara shirye-shirye na musamman a gidajen rediyo da talabijin na cikin gida domin ilmantar da jama’a kan damar da ke akwai.

A nata bangaren, Hajiya Amina Abdulmalik ta ce manufar ziyarar ita ce neman haɗin gwiwa domin ƙara yawan masu amfana da shirye-shiryen NEPC.

Advertisement

Ta ce NEPC na da shirye-shiryen horarwa da wayar da kai, amma haɗin gwiwa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai zai ƙara taimaka wa wajen isar da saƙo ga jama’a kai tsaye.

“Wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen inganta harkokin fitar da kaya daga jihar Kano da kuma bunƙasa tattalin arziƙin al’ummar jihar,” in ji ta.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending