Connect with us

News

Sojojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Ta’adda 3,000, Fiye Da 12,000 Sun Miƙa Wuya A Shekaru Biyu 

Published

on

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 101 Sun Kama Wasu 182 A Cikin Mako Daya

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun kashe fiye da ƴan ta’adda 3,000 a fadin yankin Arewa tun daga shekarar 2023 zuwa watan Yuli na shekarar 2025.

Janar Musa ya bayyana hakan ne a wani taron kwanaki biyu da Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation ta shirya a Kaduna, inda ya gabatar da cikakken jawabi kan ci gaban da rundunonin tsaro suka samu a yaki da rashin tsaro a Najeriya, musamman a Arewa.

Advertisement

‎Jihohi 6 Na Arewa Za Su Kashe Sama Da Naira Biliyan 35 Kan Motoci Da Gidajen Baƙi

A cewar Janar Musa, rundunonin tsaron kasar sun kuma samu nasarar karɓar tubabbun mayakan da suka kai 12,000, tare da ceto mutane fiye da 2,000 da aka yi garkuwa da su.

Ya ce, “Tun daga 2023 zuwa yau, mun kashe fiye da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga 3,000, mun kuma karɓi tubabbun da suka kai 12,000 a fadin Arewa. Haka zalika, mun kubutar da mutane fiye da 2,000 da aka yi garkuwa da su. Rundunonin tsaro sun kuma ƙwato bindigu sama da 2,300 da harsasai sama da 72,000 daga hannun miyagu.”

Advertisement

Janar Musa ya ce bisa tsarin inganta ƙwarewar dakarun tsaro, an kafa cibiyar koyar da dabarun yaki da sashen horarwa a babban birnin tarayya Abuja, wanda ke horar da dakaru kan dabarun yaki da gudanar da hadin gwiwa tsakanin sassan tsaro.

Ya bayyana cewa dakaru sama da 800 sun riga sun kammala wannan horo na musamman, yayin da wasu kuma ke ci gaba da samun horo a sansanonin horaswa na Jaji da Nasarawa.

Advertisement

Babban hafsan ya ce a wani mataki na sake fasalin rundunonin tsaro, an sauya sunan Operation Hadin Kai zuwa Operation FANSAN YAMMA a yankin Arewa maso Yamma domin kara ɗagawa da karfafa gwiwar dakarun da ke yaki da ta’addanci.

Ya kara da cewa sabbin rundunonin Defence Special Forces sun fara aiki a jihohin Kaduna da Neja, yayin da aka buɗe sabbin sansanonin soja tare da tura dakaru masu ingantaccen shiri a yankunan da ake fama da matsalar tsaro.

Advertisement

A cewar Musa, rundunar sojin kasar na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen zaman lafiya ta hanyar gasa da wasanni da kuma wayar da kan jama’a domin ƙarfafa hadin kai da fahimtar juna a tsakanin al’umma.

Janar Musa ya kuma jaddada kokarin rundunar wajen tallafa wa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar kafa makarantu, cibiyoyin horar da matasa a fannin ICT da kiwon dabbobi, musamman a yankunan da rikice-rikice suka fi shafa.

Advertisement

Haka zalika, ya jinjinawa cibiyoyin DICON da AFIT bisa gudunmuwarsu wajen bunkasa ƙere-ƙere da sabbin fasahohi da ke amfani da su a fagen tsaro a Najeriya.

Babban hafsan ya ce Najeriya na ci gaba da karfafa hulɗa da ƙasashen makwabta, inda ya bayyana cewa ya gana da hafsan tsaron Jamhuriyar Nijar a shekarar 2024 domin tattauna matsalolin da suka shafi barazanar tsaro a yankunan iyaka.

Advertisement

Janar Musa ya sanar da cewa Najeriya za ta karɓi baƙuncin taron hafsoshin tsaron nahiyar Afirka wanda aka shirya zai gudana daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Agusta, 2025, a Abuja.

Ya bayyana cewa taron zai kasance wata dama ta musamman wajen inganta haɗin gwiwar tsaro da musayar bayanai tsakanin ƙasashen Afirka domin fuskantar kalubalen tsaro da ke addabar nahiyar.

Advertisement

 

 

Advertisement

WIKKI TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending