Connect with us

News

‘Yan Sanda Sun Ceto Ɗaliban Makarantar Lauyoyi Guda Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su 

Published

on

Jami’an rundunar ‘yan sanda sun ceto ɗaliban Makarantar Koyon Lauya ta reshen Yola guda shida da aka yi garkuwa da su a ranar 26 ga Yuli, 2025, a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga jihar Anambara zuwa jihar Adamawa.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace ɗaliban ne a daren Asabar, wayewar Lahadi, a yankin iyakar Wukari da ke tsakanin jihar Taraba da Benuwai, inda wasu ‘yan bindiga suka tare su tare da yin awon gaba da su.

Advertisement

Rundunar Sojin Ruwa Za Ta Kafa Sabon Sansani A Kebbi

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai, Edet Udeme, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa an ceto ɗaliban cikin koshin lafiya ba tare da wani rauni ba.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an mika ɗaliban ga iyalansu da safiyar Juma’a, 1 ga watan Agusta, 2025.

Advertisement

“Jami’anmu sun nuna ƙwazo da jajircewa wajen kubutar da waɗannan ɗaliban ba tare da an biya ko sisi na kudin fansa ba. Za mu ci gaba da tsananta ayyukan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji Udeme.

 

Advertisement

Vanguard

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending