Connect with us

News

Gwamnan Neja Ya Bada Umarnin Rufe Tashar Badeggi FM  Bisa Zargin Tunzura Jama’a

Published

on

Bago 750x430

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM da ke Minna, bisa zargin yada shirye-shiryen da ke tunzura al’umma kan harkokin tsaro a jihar.

Gwamna Bago ya sanar da hakan ne a daren Jumu’a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC reshen jihar, wanda aka gudanar a fadar gwamnati da ke Minna, babban birnin jihar.

Ra’ayin Minista Ata Kan 2027 A Kano : Tawa Mahangar

Sanarwar da mai magana da yawunsa, Bologi Ibrahim, ya fitar ta ce gwamnan ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne domin kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.

“Ayyukan gidan rediyon sun kauce wa ka’ida. Yana zuga jama’a tare da haddasa rashin zaman lafiya. Gwamnati ba za ta zuba ido ba yayin da wasu ke amfani da kafafen watsa labarai wajen tayar da fitina,” in ji sanarwar.

Bayan haka, Gwamna Bago ya soke takardar shaidar mallakar filin da gidan rediyon ke kai, yana mai jaddada cewa za a dauki matakin doka kan duk wanda aka samu da laifin tayar da zaune tsaye.

Haka zalika, ya umurci Kwamishinan ‘Yan Sanda da Kwamishinan Harkokin Tsaron Cikin Gida na jihar da su gaggauta kulle gidan rediyon tare da gudanar da bincike kan mallakar gidan da ayyukan da yake gudanarwa.

Advertisement

Gwamnan ya ce dole ne a tabbatar da cewa kafafen yada labarai suna aiki daidai da ka’idojin da suka dace domin gudun haddasa fitina ko tada hankalin al’umma.

 

STALLION TIMES

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending