Connect with us

News

An Damke Mace Dauke Da Kayan Sojoji Da Alburusai A Katsina

Published

on

sr file 2025 08 05T074549.595

Rundunar hadin gwiwa da ke gudanar da atisayen tsaro na Operation Fansan Yanma ta samu nasarar cafke wata mata dauke da kayan sojoji da mujallun alburusai a garin Malumfashi da ke jihar Katsina.

Jaridar Sahara reporters ta ruwaito cewa cewa an cafke matar ne da misalin karfe ɗaya na dare a wani shingen bincike na dakarun tsaro, yayin da take kokarin ficewa daga garin cikin yanayi mai daukar hankali.

Jami’an Kwastam Sun Kwace Tsuntsaye Masu Rai 1,620 Da Aka Yi Niyyar Kai Su Kuwait

Binciken da jami’an tsaro suka gudanar a jakar matafiyar ta ya bayyana cewa tana dauke da rigar soja, wando camouflage, jaket mai atisaye, wayoyi da dama, da kuma mujallun harsasai guda uku da ke cike da alburusai.

Wata majiya daga rundunar tsaron da ta wallafa bayani a dandalin X (tsohon Twitter) a daren Litinin, ta ce an tsare matar kuma ana ci gaba da yi mata tambayoyi don gano dalilinta na mallakar kayan soja da kuma ko tana da alaka da wasu miyagun kungiyoyi.

Har yanzu ba a fitar da sunanta ko wata sanarwa ta hukuma dangane da alakar ta da wata kungiya ba, amma majiyoyi na zargin cewa tana iya kasancewa cikin wani gungu da ke da hannu wajen safarar makamai da kayan sojoji zuwa hannun ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke ci gaba da kokarin murkushe ayyukan ‘yan bindiga da masu tada kayar baya a yankunan arewacin ƙasar nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending