Connect with us

News

WAEC 2025: Fiye Da Dalibai Miliyan 1.2 Sun Gaza Samun Kiredit Biyar

Published

on

WAEC Ta Sanar Da Sabon Tsarin Gyara Jarrabawar Da Mutum Ya Fadi Ba Sai Ya Yi Jiran Shekara Daya Ba

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta fitar da sakamakon jarabawar shekarar 2025, inda aka samu gagarumar faɗuwar nasara a tsakanin ɗaliban da suka rubuta jarabawar a Najeriya da wasu ƙasashe da ke amfani da manhajar ilimin Najeriya.

Shugaban hukumar WAEC a Najeriya, Mista Amos Dangut, shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a Legas a ranar Litinin. A cewarsa, daga cikin dalibai 1,969,313 da suka rubuta jarabawar a tsakanin watan Afirilu da Yuni na wannan shekarar, 754,545 kacal ne – wato kaso 38.32% – suka samu kiredit biyar zuwa sama ciki har da darussan Lissafi da Turanci.

Jami’in NSCDC Ya Rasa Ransa A Hannun ’Yan Daba A Kasuwar Jigawa 

Wannan na nufin an samu raguwar kaso 33.8% na ɗaliban da suka yi nasara idan aka kwatanta da shekarar 2024, inda kaso 72.12% ne suka samu irin wannan nasara.

Daga cikin waɗanda suka rubuta jarabawar a Najeriya da wasu makarantu a ƙasashen Benin, Kwadebuwa da Equatorial Guinea – waɗanda ke amfani da tsarin ilimin Najeriya – dalibai 1,973,365 ne suka yi rajista daga makarantu 23,554.

Mista Dangut ya ƙara da cewa daga cikin waɗanda suka rubuta jarabawar, dalibai 1,718,090 ne – wato kaso 87.24% – suka samu kiredit biyar zuwa ƙasa, ciki har da darasin Lissafi da Ingilishi.

Hukumar ta WAEC ta ce an saki sakamakon dalibai 1,517,517 – kaso 77.06%, yayin da dalibai 451,796 – kaso 22.94% ke da wasu darussa da ba a saki ba saboda dalilai na fasaha ko sauran matsaloli da ake ci gaba da warwarewa.

Advertisement

 

 

PREMIUM TIMES 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending