News
‘Kashi 70% Na Mazabata Na Hannun Ƴan Bindiga’ – Ɗan Majalisa
Ƴan bindiga sun kashe jami’an tsaro 13 a mazabar Adabka, ƙaramar hukumar Bukuyum ta Kudu a jihar Zamfara, a wani hari da suka kai ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce bayan kisan, maharan sun hana jami’an tsaro da na ceto shigar wurin domin kwashe gawarwakin.
Ɗan majalisar jihar mai wakiltar Bukuyum ta Kudu, Hamisu A. Faru, ya shaida wa BBC Hausa cewa al’ummar yankin sun shiga cikin halin tsoro da tashin hankali bayan kisan.
“Musamman ganin waɗanda suke taimaka musu wajen kariya ne aka kashe. Ka ga ke nan me ya rage? Sai gudun hijira. Dama tuni wasu sun gudu zuwa Zuru,” in ji shi.
Faru ya bayyana cewa kusan kashi 70 cikin 100 na mazabar Bukuyum ta Kudu na ƙarƙashin ikon ƴan bindiga.
Ya roƙi gwamnatin tarayya da ta gaggauta tura jiragen yaƙi domin luguden wuta a dazukan da ake zargin maharan ke fakewa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
