News
Jami’an NDLEA Sun Kama Mutane 49 Da Ake Zargi Da Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Kano
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta ce ta kama mutane 49 da ake zargi da hannu a safarar da kuma amfani da miyagun ƙwayoyi a cikin wani samame na kwanaki biyu a jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ASP Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar .
Majalisar Dattawa Na Duba Yiwuwar Baiwa Jami’an Tsaro Damar Kada Kuri’a Kafin Ranar Zaɓe
Ya ce an gudanar da samamen ne a ranar 7 da 8 ga watan Agusta, 2025, a wurare daban-daban da ake zargin sun daɗe suna zama maboyar masu safarar ƙwayoyi.
Wuraren sun haɗa da Massallacin Idi, Fagge Plaza, Kofar Mata, Kofar Wambai, Kofar Dan’agundi, Makabartar Dan’agundi, Ladanai, Zage, da Tashar Rimi a kasuwar Rimi. Haka kuma, hukumar ta kai samame a tashar Kano Line da Tashar Rami da ke Na’ibawa, inda aka kama fiye da mutum 15.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun waɗanda aka kama sun haɗa da tabar wiwi, magungunan Pregabalin da Diazepam, codeine, Rohypnol, da ƙwayar “Suck and Die”, tare da makamai na gida.
Hukumar ta yi gargadin cewa ba za ta yi sassauci ba wajen ganin ta kawar da miyagun ƙwayoyi daga cikin al’umma. Ta kuma shawarci duk wanda ke hannu a wannan haramtaccen aiki da ya daina, kafin ya gamu da hukunci a gaban kotu.
ASP Maigatari ya ƙara da cewa bincike na ci gaba, kuma duk wanda aka samu da hannu za a gurfanar da shi bisa ƙa’ida.
