Connect with us

News

Shugaba Tinubu Zai Ziyarci Ƙasashe  Uku

Published

on

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu zai bar Abuja gobe Alhamis, 14 ga watan Agusta 2025, domin fara ziyarar aiki zuwa ƙasashen Japan da Brazil, inda kafin nan zai tsaya a birnin Dubai na Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) don wata tattaunawa ta musamman da abokan hulɗa na yankin Gulf.

Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar ta bayyana cewa, ziyarar na da nufin ƙarfafa dangantakar diflomasiyya, haɓaka tattalin arziƙi, da jawo hankalin masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Manyan Makarantun Gaba Da Sakandare Na Tsawon Shekaru Bakwai

A cewar sanarwar, shugaba Tinubu zai gana da manyan shugabanni, ‘yan kasuwa da abokan ci gaba, inda za a tattauna batutuwan kasuwanci, musayar fasaha, bunƙasa ababen more rayuwa, da haɗin gwiwa a fannoni masu muhimmanci kamar makamashi, noma da ilimi.

A Japan, ana sa ran Tinubu zai gana da Firaminista Fumio Kishida, tare da halartar tarukan kasuwanci don zurfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Japan.

Advertisement

A Brazil kuwa, tattaunawar za ta fi karkata ne kan faɗaɗa haɗin gwiwar ƙasashen Kudanci, da ƙarfafa musayar al’adu da dangantakar tattalin arziƙi.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce wannan tafiya na cikin shirye-shiryen ketare na gwamnatin Tinubu, domin mayar da Najeriya ginshiƙi a harkokin tattalin arziƙin duniya, tare da neman ƙasashen da za su tallafa wa manufofin Renewed Hope Agenda na gwamnatinsa.

Advertisement

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa Shugaban Ƙasa ba shi da lafiya, lamarin da Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta, tana mai cewa babu gaskiya a wannan jita-jita.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending