Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Manyan Makarantun Gaba Da Sakandare Na Tsawon Shekaru Bakwai

Published

on

Shugaba Tinubu ya bayyana makomar TETFUND da NITDA da NASENI

Gwamnatin Tarayya ta amince da dakatar da kafa sababbin makarantun gaba da sakandare na tarayya a duk faɗin ƙasar na tsawon shekaru bakwai.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a ranar Laraba.

Advertisement

Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano

Ministan ya bayyana cewa matakin na da nufin magance manyan matsalolin da sashen ilimi ke fuskanta, musamman a manyan makarantun tarayya. Ya ce gwamnati za ta mayar da hankali ne kan gyara da inganta cibiyoyin da ake da su, tare da dawo da martabarsu domin su yi aiki daidai da bukatun wannan zamani.

Alausa ya ce: “Kalubalenmu a yanzu ba ƙarancin damar shiga makarantu ba ne, illa dai yawan kafa sababbin cibiyoyi ba tare da inganta waɗanda ake da su ba. Wannan ya haddasa matsalar gine-gine marasa inganci da ƙarancin ma’aikata. Yanzu gwamnati za ta mai da hankali wajen tabbatar da cewa makarantunmu suna aiki yadda ya kamata, tare da ba su damar zama masu tasiri a harkar ilimi.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending