Connect with us

News

Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Nyesom Wike

Published

on

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare.

Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Ware N7.5bn Ga Hukumar Ruwa Amma Ta Kashe N1.5m Kacal A Watanni Shida

Ya kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓe mai lamba 7 a mazaɓa ta 9, Rumuepirikom, Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor.

Tsohon gwamnan jihar, ya ce zaɓen na gudana cikin lumana idan aka kwatanta da zaɓukan da suka gabata.

Advertisement

Ya bayyana cewa zaɓen Ƙananan Hukumomin ya zama dole, domin idan ba a yi shi ba, babu wanda zai shugabanci matakin ƙananan hukumomi bayan ka8rewar dokar ta-ɓaci.

Wike ya ce: “Ranar 18 ga watan Satumba dokar ta-ɓaci za ta ƙare, kuma gwamna da ’yan majalisa za su koma bakin aikinsu.

Advertisement

“Kotun Ƙoli ta soke zaɓen da ya gabata, don haka idan ba a gudanar da wannan zaɓen ba, hakan na nufin babu shugabanci a matakin ƙananan hukumomi.”

Ya kuma ƙara da cewa kayan zaɓe sun isa a kan lokaci, kuma jama’a suna kada ƙuri’arsu cikin kwanciyar hankali.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending