Connect with us

News

Gwamnan Katsina Ya Soke Lasisin Makarantun Masu Zaman Kansu A Fadin Jihar

Published

on

Majalisar dokokin Jihar Katsina ta amince da ƙirƙiro gundumomi guda shida a jihar
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Umar Dikko Radda

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Umar Dikko Radda, ya sanar da soke lasisin gudanar da harkokin dukkan makarantun masu zaman kansu da na al’umma a fadin jihar, a wani mataki na sauya fasalin tsarin ilimi.

Sanarwar ta fito ne daga Kwamishiniyar Ilimin Firamare da Sakandare, Hajiya Zainab Musa-Musawa, ta hannun mai magana da yawun ma’aikatar, Sani Danjuma, ranar Asabar a Katsina.

Advertisement

Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Nyesom Wike

A cewar Musa-Musawa, majalisar zartarwa ta jihar ta amince da wannan mataki a matsayin wani bangare na sabbin gyare-gyare a fannin ilimi, domin tabbatar da inganci, daidaito da kuma tsari mai nagarta na koyo da koyarwa a jihar.

Kwamishiniyar ta bayyana cewa wannan sabuwar doka ta yi daidai da manufar gwamnatin jihar kan makarantun kuɗi da na al’umma, wacce aka gabatar wa masu ruwa da tsaki a taron wayar da kai da aka gudanar a ranar 2 ga Yuni, 2025.

Advertisement

“Mun kuduri aniyar karfafa sa-ido da gaskiya a fannin ilimi. Wannan mataki na daga cikin hanyoyin kare makomar ‘ya’yan Katsina ta hanyar tabbatar da tsarin karatu da ya dace da ƙa’idojin duniya,” in ji Musa-Musawa.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending