Connect with us

News

Babu Takamaimen Lokacin Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro  —Gwamnan jihar Katsina Umar Dikko

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Radda kuma shugaban Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yamma a wani zantawa da aka yi da shi a BBC ya bayyana cewa babu wani lokaci da aka ƙayyade don kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a yankunan Arewa maso yammacin Najeriya.

Advertisement

Gwamna Radda ya ce dole zai ɗauki lokaci kafin a nemo mafita mai ɗorewa ga matsalolin tsaro da ake fama da su .

Kasar Burkina Faso ta sake dakatar da wasu kafafen yada labarai

Haka kuma ya ƙara da cewa, ta hanyar ƙirƙirar sabbin fasahohi, za a sami ci gaba wajen yaƙi da ƴan fashi da sauran masu laifuka.

Advertisement

Wikki Time ta ruwaito cewa Gwamna Radda ya kuma yi tsokaci game da taron tsaro da suka gudanar a kasar Amurka, inda ya ke bayyana cewa za a sami tallafi da kuma haɗa bayanan sirri ta hanyar samun tallafi daga ƙasashe irin su Amurka.

Ya kuma ƙara da cewa a yayin taron an sanar da su sabbin dabarun da za a bi wajen yaƙi da tsaro, inda ya ce sun samu ƙarin haske fiye da wanda suka sani, wanda ya ce za su yi amfani da su da zarar sun dawo ƙasa Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending