News
Rashin Tsaro Ya Tilasta Fiye Da Yara Miliyan 10 Daina Zuwa Makaranta A Najeriya
Fiye da yara miliyan 10 a Najeriya ba sa zuwa makaranta, inda mafi yawan su ke zaune a yankin Arewa da ke fama da matsalar tsaro.
Rahotanni sun nuna cewa da dama daga cikin yaran sun fice daga makarantu ne saboda rikice-rikicen da suka hada da hare-haren Boko Haram, ‘yan bindiga, da satar mutane da ke ci gaba da addabar sassan Arewa maso Gabas.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa daga shekarar 2012 zuwa 2016 an kashe malamai sama da 600 a yayin da suke aiki, yayin da sama da makarantu 1,500 aka lalata tun lokacin barkewar rikicin Boko Haram.
Yara suna cikin hadari
Binciken LEADERSHIP ya bayyana cewa sama da kashi 60 cikin 100 na yaran da ba sa zuwa makaranta na zaune a yankin Arewa maso Gabas, inda ake fama da rikici, talauci da kuma matsalar samun mafaka.
A cewar Misis Peace Pernam, kwararriya a fannin ilimi da ke Jos, “Ilimi hanya ce da ke fitar da al’umma daga talauci da rashin tsaro. Amma a Arewa maso Gabas, yara na fuskantar cikas saboda rashin shugabanci nagari da kuma karancin zuba jari a bangaren ilimi.”
Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce Najeriya ce ke da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta fiye da kowacce kasa a duniya.
Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar
A kwanan nan, Hukumar UBEC ta ce tana kokarin fadada rajistar yara domin rage yawan wadanda ba sa zuwa makaranta, musamman a yankunan karkara.
Babbar sakatariyar hukumar, Aisha Garba, ta ce galibin yaran da ke zaman gida ba tare da zuwa makaranta ba, ‘ya’yan talakawa ne da ke fama da matsalolin tattalin arziki.
Haka kuma, an kaddamar da wani shiri mai suna Lumina Programme, domin koyar da karatu da lissafi ga yara mata a yankunan da ke da wahalar samun ilimi.
Jihohi na kara zuba jari
Wasu jihohi kamar Kaduna, Kano, Jigawa da Enugu sun kara yawan kudin da suke ware wa ilimi a kasafin kudinsu, inda suka kai fiye da kashi 26 cikin 100 a shekarar 2025.
Mukaddashin shugaban hukumar SUBEB ta Kaduna, Mubarak Muhammad, ya ce gwamnatin jihar za ta horas da mambobin kwamitin kula da makarantu har 8,700 domin inganta ilimi
A bangaren kungiyoyi masu zaman kansu kuwa, IA-Foundation ta tara Naira miliyan 30 a wani taron agaji da aka gudanar a Landan domin tallafawa yaran da ke zaman gida ba tare da zuwa makaranta ba.
Masana na kiran daukar matakin gaggawa
Masana da masu sharhi sun ce idan har ba a dauki matakin gaggawa ba, to Najeriya na fuskantar barazanar faduwar tattalin arziki da ci gaba da yaduwar jahilci da rashin tsaro.
Ahmed Idris, wani masani kan al’amuran yau da kullum, ya ce “Yara da dama ba sa zuwa makaranta saboda nisan da ke tsakaninsu da makaranta, ko kuma rashin malamai. Gwamnati ya kamata ta mayar da hankali kan ilimi kyauta da amfani da fasaha wajen saukaka karatu.”
Shi ma wani malami daga Abuja, Malam Peter Ojo, ya ce dole ne a ba da fifiko ga ilimi idan ana so a samu zaman lafiya da cigaba a kasar.
Ya ce Najeriya na ware kashi 7.3 cikin 100 na kasafin kudinta ga ilimi, yayin da hukumar UNESCO ke bada shawarar a ware akalla kashi 15 zuwa 20 cikin 100.
