News
Karancin Azuzuwa Na Barazana Ga Ingancin Koyo Da Koyarwa A Islamiyyar Hayatuddeen
Shugaban makarantar Islamiyya ta Hayatuddeen da ke ƙaramar hukumar Rogo a Jihar Kano, Malam Aminu Garba, ya bayyana cewa ƙarancin ajujuwa na jefa ɗalibai cikin mawuyacin hali, lamarin da ke hana samun ingantaccen koyo da koyarwa a makarantar.
Ya bayyana haka ne a lokacin da Jami’in Yaɗa Labarai na ƙaramar hukumar Rogo, Abdu Bako Abdullahi, ya kai ziyarar aiki domin duba halin da makarantar ke ciki.
Rashin Tsaro Ya Tilasta Fiye Da Yara Miliyan 10 Daina Zuwa Makaranta A Najeriya
A cewarsa, “Yanzu haka muna da ɗalibai sama da dubu biyu, amma ajujuwan da muke da su ba su kai yadda ya kamata ba. Wannan cunkoso yana rage fahimta ga ɗalibai, kuma malamai ba sa samun damar koyar daidai.”
Malam Aminu ya ce ya kamata gwamnati da al’ummar yankin su haɗa kai wajen tallafa wa makarantar da sabbin ɗakunan karatu da sauran kayan aiki, domin ceto makomar ilimin yara a yankin.
Ya jinjinawa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar da yake bai wa harkar ilimi a jihar, musamman yadda ya ke bin sawun tsohon gwamna Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wajen inganta ilimi.
Sannan ya gode wa Kwamitin Kyautata Da’a (CRC) na ƙaramar hukumar Rogo bisa gyaran wasu ajujuwan makarantar, da ya ce sun taimaka wajen rage cunkoso.
Haka kuma ya yabawa ƙoƙarin gwamnatin ƙaramar hukumar Rogo ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abubakar Mustapha Rogo, bisa shirin gina sabbin ajujuwa a makarantar.
Baya ga haka, shugaban makarantar ya nuna godiya ga tsofaffin ɗalibai da suka gina ajujuwa guda biyu tare da gyaran bandaki, wanda ya ce zai taimaka wajen tabbatar da tsafta da kiyaye lafiyar ɗalibai.
A ƙarshe, Malam Aminu Garba ya roƙi masu hannu da shuni da sauran al’ummar gari da su taimaka wajen bunƙasa makarantar domin ciyar da ilimi gaba a yankin Rogo.
