Connect with us

News

Gwamnatin Kano Za Ta Fitar Da Sama Da Naira Biliyan 20 Don Ayyuka A Fadin Jihar

Published

on

Abba

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da fitar da sama da Naira biliyan 20 domin aiwatar da manyan ayyuka a kananan hukumomi daban-daban na jihar.

Majalisar Zartarwar jihar ce ta amince da wannan kuduri a wani taron ta na musamman da aka gudanar ranar Alhamis, 22 ga Mayu, 2025, a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Advertisement

Karancin Azuzuwa Na Barazana Ga Ingancin Koyo Da Koyarwa A Islamiyyar Hayatuddeen

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce daga cikin ayyukan da za a aiwatar har da:

Advertisement

Kammala titin kilomita biyar a Bebeji da zai ci kusan Naira biliyan 3.2;

Titi a Tudun Wada da zai ci fiye da Naira biliyan 4.6;

Advertisement

Titi a Garun Mallam da zai ci Naira biliyan 4;

Titi a Madobi da zai ci Naira biliyan 4.1;

Advertisement

Sabuwar hanya a Tsanyawa da za ta ci Naira biliyan 3.4.

Kazalika, gwamnati za ta gina sabon dakin taro a hedikwatar NLC da ke kan titin Katsina, wanda za a sanya wa sunan tsohon gwamnan Kano, marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi. Za a kashe Naira miliyan 284 a aikin.

Advertisement

Ayyukan jin ƙai da na addini:

Gwamnatin za ta kuma gina masallaci, makarantar Islamiyya da rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana a Tiga Gadan da ke karamar hukumar Gezawa da kudin Naira miliyan 151.8.

Advertisement

Taimako ga masu fama da ambaliya:

Majalisar ta nuna alhini kan asarar da ambaliya da iska suka haddasa a ƙananan hukumomin Sumaila da Doguwa, tare da kafa kwamitin tantance barnar da bayar da shawarwari kan taimako.

Advertisement

Zawaciki na cikin bincike:

An kuma tattauna halin da dakin yanka na Zawaciki ke ciki, inda aka kafa kwamitin bincike domin gano matsalolin da suka dabaibaye cibiyar, tare da la’akari da gina sabon dakin yanka na zamani don samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending