News
Shugaban Ghana Ya Tsige Alkalin Alkalan Kasar
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya tsige babbar alkalin alkalan kasar bayan wani bincike da aka gudanar ya same ta da laifin amfani da ofishinta ta hanyoyin da basu dace ba.
Gertrude Araba Torkonoo, mai shekaru 61, mace ta uku da ta shugabanci babbar kotun Ghana, an dakatar da ita daga mukamin da ta dare tun a shekarar 2023 bayan an shigar da kara a kanta.
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Mutum Biyu Da Bindigar GPMG, Harsashi 1,295 A Katsina
Shugaba John Mahama ya kafa wani kwamiti mai mutane biyar karkashin wani alkalin kotun kolin domin gudanar da bincike kan korafe-korafen da suka hada da zargin karya bayanan shari’a da kuma karkatar da kudaden al’umma.
Hukumar ta gano cewa an kafa dalilan aikata laifukan da ake zarginta an kuma ba da shawarar tsige ta daga mukaminta, in ji sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar.
Wannan dai shi ne karon farko da aka binciki wani alkalin alkalai a Ghana tare da kora. Mahama, wanda ya hau karagar mulki a watan Janairu, ya sha alwashin magance cin hanci da rashawa a kasar dake yammacin Afirka.
-
News21 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
