News
An Kama Uba da Ɗansa Bisa Zargin Cin Zarafin ’Yar Shekara 13 A Gombe
Jami’an Hukumar Tsaro ta Fararen Kaya (NSCDC) a Jihar Gombe sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari, cikin birnin Gombe.
Rahotanni na nuni da cewa an gabatar da waɗanda ake zargin a gaban hedikwatar hukumar da ke Gombe a ranar Litinin.
An Kama Uba da Ɗansa Bisa Zargin Cin Zarafin ’Yar Shekara 13 A Gombe
Mai magana da yawun NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa uban da ɗan nasa sun aikata laifin ne a lokuta daban-daban.
A cewarsa, Ibrahim Haruna, wanda tela ne, ya aikata laifin a shagonsa na ɗinki, yayin da ɗan nasa kuma ya aikata hakan a cikin gidan da suke zaune.
“Mun kammala binciken da muke gudanarwa, kuma nan gaba kaɗan za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci,” in ji Sa’ad.
Sai dai Ibrahim Haruna ya musanta zargin da ake masa, inda ya ce bai yi wa yarinyar fyaɗe ba, sai dai kawai ya taɓa ta a cikin wasa.
Hukumar NSCDC ta bayyana cewa ta ɓoye sunan yarinyar domin kare mutuncinta, tare da bin ƙa’idojin kare haƙƙin yara da dokokin kare ’yancin ɗan Adam kamr yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito
