Connect with us

News

‎Jihar Kano Ta Saka Ranar Komawa Makarantun Firamare Da Sakandire ‎

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da jadawalin da ke nuna ranakun da za a koma makarantu na firamare da sakandare a fadin jihar domin fara sabon zangon karatu na shekarar 2025/2026.

‎A wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Malam Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu, makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi, 7 ga Satumba, 2025, yayin da Sauran Makarantun za su fara karatu a ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025.

Advertisement

‎Sanarwar ta bukaci iyaye da masu kula da yara da su dauki wannan jadawalin da muhimmanci tare da tabbatar da ganin ’ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci. Haka kuma ta gargadi dalibai da za su yi sakaci cewa za a dauki matakan ladabtarwa a kansu.

Da Katin Zabe Zaku Iya Sauya Shugaba, Ku Zabi Wanda Kuke So – Inji Gwamnan Nasarawa

‎Kwamishinan Ilimi na jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ya yi fatan alheri ga malamai da dalibai a sabon zangon karatu, tare da jaddada cewa ma’aikatar za ta ci gaba da gudanar da bincike da sintiri domin tabbatar da halartar malamai da ingancin darussa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending