Connect with us

News

Da Katin Zabe Zaku Iya Sauya Shugaba, Ku Zabi Wanda Kuke So – Inji Gwamnan Nasarawa

Published

on

Advertisements
Advertisements
Spread the love

DAGA ZUBAIRU M. LAWAL

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya ce katin zabe shi ne makamin da ’yan kasa za su iya amfani da shi wajen sauya shugabannin da ba su gamsu da su ba, su kuma zabi wanda suke so.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin  mataimakinsa, Dr. Emmanuel Akabe, yayin wani gangamin wayar da kan jama’a kan muhimmancin yin rijistar katin zabe, wanda Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa, Alhaji Aliyu Bello, ya shirya a harabar ofishin jam’iyyar ranar Talata.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun Mauludi

“Mutum ba zai ce yana son wani shugaba ko ya ki wani ba, alhali ba shi da katin zabe. Wannan yaudara ce. Don haka ina kira ga jama’a su tafi su yi rijistar katin zabe domin tabbatar da ’yancinsu,” inji Gwamna Sule.

Ya kara da cewa katin zabe shi ne ’yancin dan kasa, saboda shi ne ke bashi damar kada kuri’arsa ga wanda ya cancanta ba tare da la’akari da addini, kabila ko gari ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending