News
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Mutane Tara Da Harsasai 4,264 Da Makamai A Nasarawa
DAGA ZUBAIRU M. LAWAL, LAFIA
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta kama mutum tara tare da kwato manyan makamai da harsasai 4,264 a cikin jerin samame da ta gudanar a sassan jihar.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Shattima Mohammed, ne ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a ofishin rundunar da ke Lafia, babban birnin jihar, ranar Lahadi.
MARKAZU SHIFA’UL ASQAM : Cibiyar Maganin Gargajiya ta Musulunci (Natural Islamic Herbal Center)
A cewarsa, rundunar ta samu wannan nasara ne sakamakon bayanan sirri da ta karɓa daga al’umma da kuma jajircewar jami’anta wajen yaƙi da laifuka.
CP Mohammed ya ce a ranar 7 ga Satumba, 2025, jami’an rundunar sun samu sahihan bayanai cewa wasu da ake zargin masu safarar makamai daga jihar Benue sun isa wani daji da ke iyakar Kadarko a ƙaramar hukumar Keana, inda suka sauke makamai da harsasai domin rarrabawa.
“Da jami’anmu suka isa wurin, masu safarar makaman sun gudu, amma mun kwato makamai masu yawa da suka haɗa da bindigogi AK-49 guda huɗu, AK-47 guda uku, bindiga G3 guda ɗaya, bindiga ƙarama (Sub-Machine Gun) guda ɗaya, mujallu harsasai guda 11, harsasai 7.62mm guda 4,046, harsasai 5.5mm guda 11, harsasai 38mm guda 132 da harsashi guda 75,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa a wani samame da aka gudanar ranar 6 ga Satumba, jami’an ‘yan sanda sun cafke wani mutum mai suna John Paul daga Abuja a tashar motar Akwanga-Wamba yayin da yake kan hanyarsa zuwa Abuja. A jikinsa an gano bindigogi biyar kirar gida, inda kuma ya bayyana cewa yana da abokan harkarsa da ke ci gaba da ɓoye.
Haka kuma, jami’an rundunar na ofishin ‘E’ Division a Shabu, cikin Lafia, sun kama wasu manyan masu ƙera bindigogi biyu, James Philip da Alpha Philip, dukkansu daga unguwar Faferuwa.
Bincike ya kuma kai ga kama wasu mutane da ake zargi da hannu wajen siyar da makaman, waɗanda suka haɗa da:
Usman Abubakar daga Shendam Road, Lafia, Yakubu Danladi daga Mararaba Akunza, Lafia, Usman Kasimu (wanda aka fi sani da Bobo) daga Bukan Sidi, Lafia, Abdullahi Adamu daga Bukan Sidi, Lafia.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun haɗa da bindigogi dogaye guda 13, bindigogi ƙanana guda 10, bindiga Revolver guda ɗaya, takuba guda uku, rigunan sanye da huluna na ‘yan sanda guda uku, injinan ƙera bindiga guda uku da wasu kayan aiki.
CP Mohammed ya yabawa jajircewar jami’ansa, tare da tabbatar wa jama’a cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawar da miyagun mutane daga Nasarawa.
Ya ce, “Ina kira ga kowa ya kasance mai lura, ya kasance mai bin doka, kuma ya rika bayar da bayanai ga rundunar domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.”
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
