News
Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutum Daya, Ta Yi Awon Gaba Da Uwa Da Ɗanta A Zariya
Wani mutum ya rasa ransa, yayin da wata uwa da ɗanta ƙarami suka bace sakamakon ruwan sama mai tsananin ƙarfi da aka tafka a garin Zariya dake Jihar Kaduna.
Shaidu a unguwar Tudun Jukun sun bayyana cewa ruwan ambaliyar ya tafi da mutane da dama, inda aka gano gawar wani matashi mai suna Yusuf Surajo, wanda aka fi sani da Abba. Amma har yanzu ba a gano uwa mai suna Fatima Sani Danmarke da ɗanta mai shekaru uku ba, da kuma wani mai babur da ya afka cikin ruwan.
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Mutane Tara Da Harsasai 4,264 Da Makamai A Nasarawa
Wani mazaunin yankin, Mustapha Badamasi Dan Bakano, ya ce“Mun gano gawar mutum ɗaya, amma mutum uku har yanzu ba a gano su ba. Wannan al’amari ya tayar mana da hankali matuƙa.”
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ta ce tana jiran ƙarin bayani daga ofishinta na Zariya.
Mai magana da yawun hukumar na wucin gadi, Dominic Philip, ya shaida Jaridar LEADSHIP cewa “Mun riga mun tura jami’anmu daga ofishin Zariya zuwa wurin da abin ya faru. Amma a yanzu ba mu da cikakken bayani kan adadin mutanen da abin ya shafa.”
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
