News
Babban Layi Na Wutar Lantarki Ya Sake Faɗuwa
Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya sake faɗuwa a ranar Laraba, abin da ya haifar da katsewar wuta a wasu sassan Najeriya.
Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki ta ce ƙarfin wutar ya ragu daga 2,917 megawatts zuwa 1,500 megawatts tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na rana.
Jami’an Ƴan Sanda Sun Cafke Masu Fashi Uku A Kano, Sun Gano Motar Da Aka Sace A Abuja
Kamfanin Rarraba Wuta na Abuja (AEDC) ya tabbatar da faruwar matsalar, inda ya ce ta samo asali ne daga layin ƙasa da ya fadi da misalin ƙarfe 11:23 na safe.
A wani saƙo da kamfanin ya aike wa kwastomomi, AEDC ta ce:
“Rashin wutar da ake fuskanta yanzu ya faru ne saboda matsalar da ta shafi babban layin ƙasa. Wannan ya janyo yankunan da muke rarraba wuta suka shiga duhu. Muna aiki tare da hukumomin da suka dace domin dawo da wutar da zarar an shawo kan matsalar. Mun gode da haƙurinku.”
Wannan katsewar wuta na zuwa ne a wani lokaci da ‘yan Najeriya ke ta kukan rashin samun wutar lantarki mai ɗorewa, lamarin da ya kara ta’azzara rayuwar yau da kullum da harkokin kasuwanci.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
