News
Cutar Gambon Fatar Jiki Ta Yi Ajalin Mutum 8 A Adamawa
Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar mutane takwas sakamakon bullar wata cuta da ake zargin Buruli ulcer wato cutar gambon fatar jiki a ƙauyen Malabu, ƙaramar hukumar Fufore.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Felix Tangwami, ne ya bayyana hakan wa manema labarai a Yola ranar Talata. Ya ce wasu daga cikin waɗanda cutar ta shafa na karɓar kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama (MAUTECH).
Dakta Tangwami ya ce an ɗauki samfurin cutar daga wajen marasa lafiya domin gwaji, kuma aka aika shi zuwa Dakin Gwaje-gwajen Ƙasa don gudanar da bincike.
Ya ƙara da cewa jami’an lafiya sun sanya al’ummar da abin ya shafa a ƙarƙashin kulawa ta musamman, domin hana yaduwar cutar zuwa ƙauyukan da ke makwabtaka.
“Gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Ƙasa, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da wasu abokan hulɗa, sun ɗauki matakan gaggawa don dakile cutar,” in ji shi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
