Connect with us

News

Jami’an Ƴan Sanda Sun Cafke Masu Fashi Uku A Kano, Sun Gano Motar Da Aka Sace A Abuja

Published

on

Rundunar ƴan sanda ta jihar Kano ta kama wasu mutum uku da ake zargi da fashi da makami tare da gano wata mota kirar Toyota Corolla S, 2014 model da aka sace a Abuja.

Wadanda ake zargin su ne Ismail Imran mai shekaru 20, Abdulaziz Yahaya mai shekaru 31 da Musa Ibrahim Isah mai shekaru 29, dukkansu mazauna Rigasa a jihar Kaduna. An cafke su ne a ranar 6 ga Satumba, 2025, bayan wani samame da jami’an tsaro tare da hadin gwiwar sa-kai suka gudanar.

Cutar Gambon Fatar Jiki Ta Yi Ajalin Mutum 8 A Adamawa

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce binciken farko ya nuna cewa an sace motar ne a unguwar Durumi da ke Abuja a ranar 5 ga Satumba, inda masu fashin suka kai hari kan iyalan mai motar, suka kuma jikkata ɗaya daga cikinsu.

Kwamishinan ƴan sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai cewa nasarar ta tabbatar da muhimmancin tsarin community policing.

Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, sannan za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu da zarar an kammala.

Ta kuma shawarci jama’a da su rika lura tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargi, domin tabbatar da tsaro a jihar da ƙasar baki ɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending