News
NECO 2025: Nasarar Ɗaliban Kano, Mai Cike Da Kalubale
DAGA TIJJANI SARKI
Daliban jihar Kano ne suka fi kowa nasara a jarrabawar kammala sakandire ta ƙasa (NECO) ta shekarar 2025, inda rahoton hukumar ya nuna cewa ɗalibai 68,159 daga jihar sun samu credits biyar da sama, ciki har da Turanci da Lissafi. Wannan ya sanya Kano ta zama ta farko a Najeriya a bana.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa nasarar ba ta zo da sauƙi ba, illa sakamakon matakan gaggawa da gwamnati ta ɗauka bayan ta karɓi mulki a 2023.
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sakatariyar Ƴan jarida A yobe, Sun Harbe Ɗan Sanda
Ya ce gwamnatin sa ta biya kuɗin jarrabawar NECO da WAEC ga ɗalibai fiye da 141,000 da ya kai kusan naira biliyan uku, ta biya bashin jarrabawar da aka gada na sama da naira miliyan 748, ta ɗauki sabbin malamai dubban, ta gyara makarantu da kuma raba kayan karatu da uniform kyauta. Har ila yau, ya ce an ware wa bangaren ilimi kaso 31 cikin ɗari na kasafin kudin jihar na 2025, mafi girma a Najeriya.
Sai dai wannan nasara ta jawo muhawara, inda tsohon kwamishinan ilimi, Muhammad Sunusi Kiru, ya ce gwamnatin baya ce ta gina tushenta. Amma masu sharhi sun kalubalanci wannan ikirari, suna cewa a lokacin gwamnatin da ta gabata ne aka fi sayar da filayen makarantu, gine-gine suka lalace, kuma malamai suka shafe shekaru ba tare da samun ci gaba ba.
Duk da wannan nasara, kalubale na ci gaba da barazana ga ilimin jihar. Akwai makarantu da dama a ƙauyuka da ke fama da matsalar kujeru, rufin da ke zuba ruwa da kuma ɗalibai masu cunkoso.
Masu lura da harkokin ilimi na ganin wajibi ne gwamnati ta ci gaba da saka idanu kan shirin gyaran makarantu tare da haɗin gwiwar malamai, iyaye da al’umma, domin tabbatar da dorewar wannan nasara da kuma samun ci gaba mai ɗorewa.
