News
‘Yan Sanda Sun Cika Hannu Da Matar Da Ta Kona Fuskar ‘Yar Mijinta Da Tafasasshen Man Girki
Wata matar aure ta shiga hannu kan zargin ƙone fuskar ’yar mijinta, Fatima Talba mai shekara 17 da tafasasshen man girki, a unguwar Jiddari Polo da ke Jihar Borno.
Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru a ranar Asabar da ta gabata, bayan wata taƙaddama da kaure tsakanin Fatima da matar ubanta.
“Matar ce ta kwara wa Fatima man girki mai zafi a fuska, wanda ya janyo mata mummunan ƙuna,” in ji majiyar.
An bayyana cewa Fatima na tare da mahaifinta a lokacin da suke shirye-shiryen aurenta da ake sa ran yi a nan gaba.
Bayan faruwar lamarin, an garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), inda ta ke kwance a sashen kulawa ta musamman.
“Halin da Fatima ke ciki ya tsananta, fuskarta ta ƙone sosai,” cewar majiyar.
Kakakin rundunar ’yan sandan Borno, Nahum Dado, ya tabbatar da cewa an kama matar da ake zargi da aikata laifin.
Jama’ar unguwar sun tausaya w Fatima baya tare da kira ga hukumomi da su tabbatar da an yi mata adalci.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
