News
Da na so wa’adi na uku, na san yadda zan bi wajen cimma burina –Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce ba gaskiya ba ne cewa ya taɓa neman wa’adi na uku a lokacin mulkinsa, yana mai jaddada cewa da shi kansa ya so, da ya san hanyar da zai bi ya cimma burinsa.
Obasanjo ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba, a wani taron tattaunawar dimokuraɗiyya da Gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a Accra, babban birnin Ghana.
Ya ce babu wani ɗan Najeriya, mai rai ko mamaci, da zai iya tabbatar da cewa ya taɓa faɗa masa yana son wa’adi na uku.
“Ina da hankali. Da na so wa’adi na uku, na san hanyar da zan bi wajen samunsa. Kuma babu wani ɗan Najeriya – mai rai ko mamaci – da zai iya cewa na taɓa faɗa masa ina neman wa’adi na uku,” in ji Obasanjo.
‘Yan Sanda Sun Cika Hannu Da Matar Da Ta Kona Fuskar ‘Yar Mijinta Da Tafasasshen Man Girki
Ya kuma jaddada cewa manyan nasarorin da ya cimma a lokacin shugabancinsa sun fi wahalar samu fiye da wa’adi na uku, inda ya ambaci rangwamen bashi da Najeriya ta samu daga ƙasashen waje a zamaninsa.
“Da na so samun rangwamen bashi – wanda ya fi wahalar samu fiye da wa’adi na uku – na samu shi. Don haka, da na so wa’adi na uku, da na samu shi ma,” in ji shi.
