News
Yan Bindiga Sun Sace Kansiloli Biyu Da Limami A Zamfara
’Yan bindiga sun kai hari a unguwar Tsauni da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara a daren Laraba, inda suka sace kansiloli biyu daga Gidan Gona da Tsibiri a Maradun LGA tare da wani limami.
Shaidu sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a gaban gidajen wadanda aka sace, bayan sallar Magariba, yayin da maharan suka kwace wayoyin hannu daga tare da an yi musu turjiya ba.
Jami’an ‘Yansanda Sun Ƙwato Muggan Ƙwayoyi Na Naira Miliyan 120 A Kano
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tura jami’an tsaro zuwa wurin domin ceto wadanda aka sace, sannan ya bukaci al’umma da su ba da bayanai cikin gaggawa don taimakawa wajen cafke maharan.
Shugaban karamar hukumar Maradun, Sanusi Gamagiwa, ya bayyana cewa maharan sun sace mutane shida a farko, daga cikin su uku aka saki, yayin da suka bar kansiloli biyu da limamin unguwar.
Duk da haka, har yanzu ’yan bindigar ba su tuntubi kowa don bayyana bukatunsu ba, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin ceto wadandaaka sace.
