News
Yadda Wani Manomi Ya Rasa ‘Ya’yansa Biyar A Hatsarin Jirgin Ruwa
Wani manomi mai shekaru a ƙaramar hukumar Agatu ta jihar Benuwai ya shiga cikin mummunan tashin hankali bayan jirgin ruwa da yake ciki tare da ‘ya’yansa ya kife, lamarin da ya yi sanadin mutuwar yara biyar daga cikinsu.
Lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi yayin da mutumin da ‘ya’yansa shida ke dawowa daga gonar su inda suka je girbe rogo. Shaidu daga yankin sun bayyana cewa jirgin da suke ciki ya kife a tsakiyar hanya, inda dukkan su suka fada cikin ruwa.
Gwamantin Kano Ta Fitar Da Sabon Tsarin Biyan Haraji Ta Hanyar Internet
Wani mazaunin yankin mai suna Ameh ya shaida wa manema labarai cewa, “Bayan faruwar lamarin, mazauna yankin da masu nutsewa suka shiga cikin kogin domin ceto mutanen. Amma abin takaici, yara biyar sun rasu, sai mahaifinsu da ɗaya daga cikin yaran kawai suka tsira.”
Hatsarin ya tuna da wasu abubuwan da suka faru a baya a jihar. A shekarar 2024, mutane 14 ne suka mutu lokacin da jirgin da ke ɗauke da masu halartar jana’iza ya kife a kogin Buruku. Haka kuma a watan Disamba na shekarar 2024, wasu ‘yan kasuwa 20 – mafi yawansu mata da yara – sun rasu a wani hatsarin jirgin ruwa a kogin Benuwai, a yankin Agatu.Ruwa
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News18 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
