News
Kotu Ta Wanke Ango Da Ƴanuwansa 11 Daga Zargin Kashe Jami’ar Ƴan Sanda
Wata babbar kotu a birnin Fatakwal, jihar Rivers, ta wanke wasu matafiya guda 12 da ake zargi da hannu wajen mutuwar Insp. Christiana Erekere, jami’ar ƴan sanda da ke aiki a ofishin ƴan sanda na Taabaa, a ƙaramar hukumar Khana ta jihar.
Lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Afrilu, 2024, lokacin da waɗannan matafiyan ke kan hanyarsu ta zuwa bikin ɗaurin auren ɗaya daga cikinsu, Efeoghene Uwheraka, a jihar Akwa Ibom.
Gidauniyar Sallamar Barau Care Foundation Ta Raba Tallafi Ga Mata Marasa Lafiya A Kano
Rahotanni sun ce jami’an ƴan sanda ne suka tsayar da su don binciken takardun motarsu, amma abin ya rikide zuwa saɓani, wanda daga bisani ya haifar da mutuwar jami’ar ƴan sandan.
A hukuncin da Mai shari’a Augusta Chukwu ta yanke a ranar Litinin, ta bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun kasa kawo hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar cewa waɗannan matafiyan ne suka aikata laifin.
“Shaidun da aka gabatar jita-jita ne kawai, babu wata hujja mai ƙarfi da za ta tabbatar da laifin da ake tuhumarsu da shi,” in ji Mai shari’ar.
Kotun ta wanke mutum 12 ɗin gaba ɗaya daga zargi, tare da bayar da umarnin a biya kowannensu Naira miliyan ɗaya a matsayin diyyar tsare su ba bisa ƙa’ida ba na tsawon watanni 18.
Waɗanda aka wanke sun haɗa da:
Efeoghene Uwheraka, Joy Uwhereka, Shirley Wealth, Napoleon Uwhereka, Ejiro Ejogbamu, Moses Agege, Precious Iyota, Kikelomo Odusanya, Wealth Ojoh, Ighofose Oke, Blessing Ovie, da Emeka Joshua, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Sai dai ’yan uwan marigayiyar, Insp. Christiana Erekere, sun nuna rashin jin daɗinsu da hukuncin, inda suka ce za su duba yiwuwar ɗaukaka ƙara domin neman adalci ga ‘yar uwarsu.
