Connect with us

News

Gwamnatin Tarraya Na Duba Bukatar Mutane 170 Daga Kasashen Waje Da Ke Neman Zama Yan Najeriya

Published

on

Tunji Ojo

Ministan harkokin cikin gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana duba bukatun mutane 170 daga kasashen waje da ke neman samun zaman dan kasa a  Najeriya.

Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (wanda a da ake kira Twitter), inda ya ce kwamitin bada shawara kan batun zama dan kasa ne ke nazarin bukatun da kuma bada shawarar wadanda shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai amince da su.

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Ɗan Hakimi Da Jami’an Ɗan Sanda A Gombe

A cewarsa, wannan aiki wata gasa ce ta amana da gaskiya, inda gwamnati za ta tabbatar da cewa an gudanar da aikin cikin adalcI .

Ministan ya ce zama dan kasa a babbar kasa bakar fata mafi girma a duniya kamar Najeriya, babbar dama ce da ke bukatar kulawa da tunani mai zurfi kafin daukar mataki.

Ya kara da cewa, kwamitin da ke duba lamarin ya kunshi wakilai daga ma’aikatar shari’a, ma’aikatar harkokin waje, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), da kuma hukumar shige da fice ta kasa (NIS).

Tunji-Ojo ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu za ta ci gaba da kokarin inganta kasar, tare da mayar da Najeriya kasa mai jan hankalin mutane daga sassa daban-daban na duniya.

Advertisement

 

NAN

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending