Connect with us

News

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Ɗan Hakimi Da Jami’an Ɗan Sanda A Gombe

Published

on

NURTW clash

An tabbatar da mutuwar mutum biyu, ciki har da ɗan hakimi da kuma jami’an ɗan sanda, a wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a garin Komi da ke cikin karamar hukumar Funakaye ta jihar Gombe

Rahotanni daga yankin sun ce rikicin ya samo asali ne a ranar Lahadi, bayan wata muƙabala tsakanin manoma da makiyaya kan filin noma da hanyoyin kiwo, wanda daga bisani ya rikide zuwa mummunan artabu tsakanin matasa daga garuruwa makwabtaka.

Advertisement

“Idan Mijinki Baya Iya Kai Ki Awun Juna Biyu, To Ba Sonki Yake Ba” — Dr. Zainab Mu’azu

Daga cikin waɗanda suka mutu har da Mohammed Jibrin, ɗan shekara 27, wanda shi ne ɗan Hakimin Komi. An ce an garzaya da shi asibitin gwamnati na Biri, da ke karamar hukumar Nafada, bayan ya samu raunuka masu tsanani, amma daga baya ya rasu yayin da ake jinyarsa.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce manoma uku da makiyayi ɗaya sun samu raunuka, yayin da ɗan sanda ɗaya ya rasa ransa lokacin da matasa suka kai wa jami’an tsaro hari.

Advertisement

“Da jami’anmu da ’yan sa-kai suka isa wajen, wasu matasa daga ƙauyukan Dukku da Kwami suka far musu, suka kashe ɗaya daga cikin ’yan sanda,” in ji DSP Abdullahi.

Ya ƙara da cewa, an kama mutum 17 da ake zargi da hannu a rikicin, kuma yanzu haka an dawo da zaman lafiya a yankin bayan tura ƙarin jami’an tsaro.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending