News
Yan sanda uku sun shiga hannu bisa zargin lakadawa ɗan abokin aikinsu duka saboda soyayya da matar ASP
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wasu jami’anta uku bisa zargin lakadawa wani matashi mai shekara 22 mai sunansa Jacob Sunday duka har ya suma, a barikin ‘yan sanda na 22 PMF da ke Ogudu, jihar Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe shida na yamma a ranar Talata, lokacin da jami’an — Insp. John Alom daga 63 PMF Ikorodu, Insp. Sunday Adoga daga CTU Base 2 Ikeja, da Insp. Jehovah Usam daga 22 PMF Ikeja — suka jawo Jacob zuwa ɗakinsu, inda suka lakad masa duka.
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kwace Dala 49,700 Daga Hannun tsohon Kwamishinan Zaɓe
Jacob, wanda shi ɗan wani jami’i ne mai suna Inspector Sunday Ochepo, ana zargin yana soyayya da wata mata mai suna Sarah Richard, matar ASP Audu Richard, wanda shi ma ke zaune a barikin.
Majiyar ta ce jami’an sun tube matashin tsirara kafin su yi masa duka har ya suma. Daga baya, wasu ‘yan sanda masu bincike suka samu labari suka kai ɗauki, suka garzaya da shi asibitin Police College Cottage Hospital da ke Ikeja, inda yake karɓar kulawa a sashen gaggawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an uku da ake zargi yanzu suna tsare, yayin da ake ci gaba da bincike kan abin daya faru.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
