Connect with us

News

An Damfari Wata Mata Euro 3,300  Bayan Da Aka Sayar Mata Da Kokwanba A Matsayin Tsabar Zinari

Published

on

images (3)

Wata mata ‘yar garin Birgland, a gabashin Nuremberg, Jamus, ta gamu da mummunan damfara bayan ta sayi abin da ta yi imanin tsohuwar tsabar zinari ce ta musamman ta yanar gizo. Sai dai, abin da ya iso mata daga mai sayarwar shi ne Kokwamba (cucumber), maimakon tsabar zinari.

Rahotannin ‘yan sanda sun bayyana cewa matar ta ga tallan tsabar zinarin a wani shafin kasuwanci na intanet kuma ta yi mu’amala da mai sayarwar. An amince cewa za ta biya kudin ne bayan karbar kayan, amma bata kasance a gida lokacin da akwatin ya iso ba. Mahaifinta ne ya karbi kayan, kuma ba tare da bude ya duba abin da ke ciki ba, ya tura euro 3,300 ga mai sayarwar.

Yan sanda uku sun shiga hannu bisa zargin lakadawa ɗan abokin aikinsu duka saboda soyayya da matar ASP

Da yamma matar ta dawo gida ta bude akwatin, sai ta tarar da abin mamaki — Kokwamba kawai ne a ciki, ba tsabar zinari ba.

‘Yan sandan Birgland sun ce mai sayarwar da aka yi mu’amala da shi ba ya wanzu, don haka zai yi wuya a gano wanda ya damfara matar. Sun kuma gargadi jama’a da su rika taka-tsantsan wajen yin sayayya ta yanar gizo, musamman idan farashin abu yayi kama da abin al’ajabi.

 

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending