News
Trump Ya Yi Barazanar Turo Sojojin Amurka Su Mamaye Nigeria Kan Zargin Kisan Kiristoci
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar cewa ƙasarsa na iya ɗaukar matakin soja a Najeriya idan gwamnatin ƙasar ta ci gaba da barin ana kisan Kiristoci.”
Trump ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Asabar.
Gwamnatin Tarraya Ta Mayar Da Martani Kan Kalaman Donald Trump
Wannan na zuwa ne bayan da tsohon shugaban ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai matuƙar damuwa kan ‘yancin addini (Country of Particular Concern) saboda abin da ya kira “kisan gilla ga Kiristoci.”
A cikin sabon jawabin nasa, Trump ya kuma bayyana cewa Amurka za ta dakatar da duk wani tallafi da taimako da take bai wa Najeriya, matuƙar gwamnatin ƙasar ta gaza ɗaukar mataki kan abin da ya kira “ta’addanci da zalunci ga Kiristoci.”
A gefe guda, Gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwa inda ta ƙaryata zargin da Trump ya yi, tana mai cewa Najeriya ƙasa ce da ke mutunta ‘yancin addini, kuma gwamnati tana aiki don tabbatar da zaman lafiya da daidaito tsakanin al’ummomi.
Rahotannin Jaridar INDA RANKA sun nuna cewa bayan wannan jawabi, jama’a da dama a Najeriya sun rika tofa albarkacin bakinsu a kafafen sada zumunta, wasu na goyon bayan kalaman Trump, yayin da wasu ke ganin maganarsa ta cika da siyasa da son kai.
