News
Majalisar Tarayya Ta Amince Da Daurin Shekara 14 Ga Malamai Masu Lalata Da Ɗalibai
Majalisar Tarayyar Najeriya ta amince da hukuncin daurin shekara 14 ga duk wani malami da aka samu da laifin cin zarafi ko lalata da ɗalibai a makarantu, a wani mataki da ake ganin zai taimaka wajen kare ɗalibai daga cin zarafi a fadin ƙasar.
Dokar mai taken Hana Cin Zarafin Dalibai ta 2025 (HB.1597), ta samu amincewar Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa a ranar Laraba, bayan ta tsallake karatu na uku.
Hukunci mai tsanani ba zabin tara
A tanadin dokar, duk wanda aka samu da laifin:
neman jima’i daga ɗalibi, tilasta mu’amala ta jima’i, yin barazana domin cimma buƙatar jima’i, taɓa jiki ko runguma ta rashin ɗa’a, aika saƙonnin batsa, hotuna ko bidiyo, ko bibiyar ɗalibi da nufin cin zarafi,
zai fuskanci: Daurin shekara 14, Ko shekara biyar mafi ƙaranci, Ba tare da damar biyan tara ba.
Kwamitocin kula da korafe-korafe a makarantu
Dokar ta kuma tilasta wa dukkan makarantu, musamman na sakandare zuwa manyan makarantu, su kafa kwamitin zaman kansa domin karɓa da bincikar ƙorafe-korafen cin zarafin ɗalibai.
Haka kuma, an bai wa duk ɗalibin da aka ci zarafinsa damar shigar da ƙara kai tsaye ba tare da fargabar rufe bakin magana ba.
Yanzu haka dokar na jiran sahihin amincewar Shugaban Ƙasa, kafin ta fara aiki a hukumance.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
