Opinion
Koyar da ɗaliban firamare da sakandare da Hausa a Kano abu ne mai kyau, ga dalilaina – Daga Mubarak Ibrahim
Cire wajabcin koyarwa da Yaren Turanci a “primary da secondary schools” da gwamnatin Kano ta ke so ta yi zai kawo ci-gaba ga yaren Hausar, zai zama alkhairi ga masana harshen Turanci, kuma hakan zai inganta ilimi a matakin makarantun primary da secondary a jahar nan tamu mai albarka. Ga dalilaina kamar haka:
1. A yanzu Harshen Hausa shine yare na 19 a cikin yaruka 20 da suka fi yawan masu magana da su a duniya, shine yare na 1 a Afirka, bayan ya doke yaren Kiswahili/ Swahili da Wolof. Ya na da mutane kimanin miliyan 94.4 da suke magana da shi a faɗin duniya. To in gwamnatin Kano ta sahhale koyo da koyarwa da shi a matakin farko na ilimi, yaren zai ƙara samun talifai, wallafe-wallafe na fassarar iliman da a ka wallafa da Turanci kuma a ke koyar da su a waɗannan matakan na ilimi kuma da harshen Turancin. Hakan zai ƙara wa yaren, tare da al’adun Bahaushe ɗaukaka da sabbin masu koyon yaren a duniya.
Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Amfani Da Harshen Hausa A Makarantu
2. Masana Harshen Turanci na jami’a da irin masu karantar da shi a tsangayu kamar su Malam Kabiru Musa Jammaje, Malam Habibu Aminu Lawan, Dr. Anas A. Kamfa, Malam Mukhtar Hikima da sauran su, za su samu “recognition” da ya fi na yanzu, za a fi ɗaukar iliminsu da sana’arsu da mahimmanci saboda ƙarancin masana yaren da kuma damar koyar yaren, sannan za su samu “official” haɗin guiwa da makarantu ko “departments” da suka wajabta Turanci a matsayin sharaɗin samun admission.
3. Sahhale koyo da koyarwa da Hausa a waɗannan matakan zai taimakawa yara masu tasowa su fahimci ilimin da kyau. Ba kowa ne zai gane wannan ba sai malamin makarantar da ya ke fama da ɗaliban primary da secondary kan fahimtar “basics” amma ba sa iyawa saboda babu Turanci. Ba a ƙasan ba, har a saman ma a yanzu babu Turancin, kuma fannonin ilimin da a ke koyarwa da Turancin ma ba a gane su. Don haka muke rainon jahilan yara na gaske. Abin takaicin ma shine, yaran da suke karantarwar masu Diploma da NCE ɗin suma fa ƙwaryar sama ce kawai ta ke dukan ta ƙasa. Ma’ana, “da’ufaɗ ɗalibu wal maɗlub” a ke yi.
A zahirin gaskiya, tun daga 90s fa koyo da koyarwa cikin harshen Turanci ya lalace a makarantun gwamnati. Na yi LEA primary school da Secondary school a 90s, kuma, kaso mafi rinjaye na malamanmu a wancan lokacin da Hausa suka koyar da mu. Sai dai hakan bai hana ni koyon Turanci ba irin wanda Allah ya yassare min, kuma ba tare da na bar Najeriya ba, ko Arewa ma a lokacin koyonsa. Kawai dai akwai ƙaddarar rayuwa, damar da Allah ya baiwa mutum, azamarsa da kuma malamai na gari. Akwai malamina a Junior Secondary School da na sha bayar da labarinsa, wanda yayi ta yi mana taƙarar cewa har abada ba za mu iya Turanci ba tunda an haife mu a ghetto, kuma gwamnati ba ta ba su albashin da zai ishe su har su saki jiki su koya mana. Wannan a lokacin mulkin General Abacha ne. Maganganunsa irin waɗannan sun yi ma wasu da dama tasiri a ajinmu tunda sun karɓi tunaninsa har zuwa yanzu, kusan shekaru 30 bayan haka.
Na yadda rabi da rabi cewa in ka na so yaranka su iya Turanci ka kaisu makarantar da a ke magana da Turanci. Wannan kam haka ya ke a ilimin Psychology cewa ɗan Adam ya na koyon duk abinda a ke yi a kewayensa. Amma, mutum nawa ke da ikon kai yaransu makarantu masu zaman kansu da a ke sirfa Turancin? Sannan kuma, a tsawon lokutan da na karantar a makarantun gwamnati da a ke bayar da ilimi da Hausa, da kuma makarantu masu zaman kansu da a ke bayar da ilimi da Turanci, na fahimci cewa yaran makarantun gwamnatin nan sun fi fahimtar inda a ka sa gaba. Wallahi ko a jami’a da makarantun gaba da secondary irin CAS da na karantar, zaƙaƙuran yaran da na yi alfahari da su kuma na ke yi da su har yanzu, sun fi yawa a cikin waɗanda a ka koyawa da Hausa a primary da secondary schools. Waɗancan kam akwai Turanci, amma ba sa fahimta kamar ƴan makarantun “ghetto”!
Don haka, ina goyon bayan sahhale koyo da koyarwa da yaren Hausa a makarantun Primary da Secondary na Jahar nan tamu ta Kano mai albarka! Allah ya tabbatar da haka, Ya ɗaukaka yaren Hausa da Jahar Kano baki ɗaya. Amin. Mu kwana lafiya!
Mubarak Ibrahim Mazaunin garin Kano ne, kuma tsohon malamin Jami’ar Alqalam. Za a iya tuntubarsa ta:08067444787 – abusfyy@gmail.com
