Connect with us

News

Wasu Mamallaka Filaye A Dan-gwauro Sun Fara Addu’oi Kan Abunda Suka Kira Yunkurin Kwace Wurarensu

Published

on

WhatsApp Image 2025 11 08 at 15.00.11 540x430
Spread the love

Wasu mamallaka filaye a yankin Dan-Gwauro da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun fara salloli da addu’oi na musamman domin neman taimakon Allah kan abunda suka Kira yunkurin kwace wurarensu ta hanyar sake bijiro da Awon Fulotai a karo na biyar.

Wasu daga cikin mamallakan filayen da suka zanta da manema Labarai sunyi zargin cewa wasu mutane ne ke ƙoƙarin bijiro da Awon ba tare da sani ko amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf ba.

Fasinja Ya Ji Munanan Raunuka Bayan Power Bank Ya Fashe A Filin Jirgin Sama

Sun kara da cewa ana amfani da batun sauyawa kasuwar ‘Yan Lemo da ‘Yan Kaba matsuguni zuwa yankin a matsayin manufar aikin donin Fakewa a kwace filayen jama’a.

Sunce za a iya mayar da Kasuwannin zuwa yankin ba tare da an kwace haƙƙin kowa ba, tare da roƙon Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta shiga tsakani domin warware matsalar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *