News
Fasinja Ya Ji Munanan Raunuka Bayan Power Bank Ya Fashe A Filin Jirgin Sama
Wani mutum ya ji munanan raunuka a ƙafafunsa da yatsun hannunsa bayan batirin Power Bank da yake ɗauke da shi ya yi zafi har ya fashe a aljihunsa, lamarin da ya haddasa hayaki da firgici a filin jirgin saman Melbourne.
Rahotanni daga wurin sun ce lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis a dakin hutun fasinjojin ajin kasuwanci na kamfanin Qantas (Business Lounge), inda batirin ya kama da wuta, sannan ya fitar da hayaki mai yawa a cikin dakin.
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Najeriya
Sakamakon hayakin, jami’an filin jirgin sun tura mutane kusan 150 cikin gaggawa domin kare lafiyarsu. Ma’aikatan wurin sun ruga da mutumin zuwa bandaki, inda suka zuba masa ruwa daga shawa don kashe wutar, kafin jami’an lafiya su karɓi ragamar kula da shi.
An garzaya da mutumin asibiti domin ci gaba da kula da raunukan da ya samu.
Masana sun jaddada haɗarin da ke tattare da amfani da Power Bank, musamman a wuraren da mutane ke taruwa kamar filayen jirgin sama.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
