News
Shirin REA Gidauniyar M.d Abba Aliyu, Ta Tallafawa Matasa A Jihar Kano.
Shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), Injiniya M.D Abba Aliyu Abubakar, ya ƙaddamar da rabon na’urorin hasken rana (Solar) domin inganta wutar lantarki a Kano.
Taron wanda ya gudana cikin yanayi na farin ciki, ya kuma haɗa da yaye dalibai da aka horas a sana’ar haɗa Solar, tare da basu takaddar kammala horo.
Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo
A wani bangare na tallafin, Gidauniyar Abba Aliyu (Abba Aliyu Foundation) ƙarƙashin jagorancin Alhaji Da’u Aliyu Abubakar (Kogunan Kasar Hausa), ta miƙa tallafin jari ga matasan da suka kammala horon domin su fara dogaro da kansu a fannin fasahar hasken rana.
Da yake jawabi a wajen taron, MD na REA, Abba Aliyu Abubakar, ya bayyana cewa shirin wani ɓangare ne na manufar gwamnatin tarayya na ƙarfafa wutar lantarki a karkara, da kuma samar wa matasa ayyukan yi.
Ya ce: “Manufarmu ita ce mu tabbatar cewa yankunan karkara ba su bar baya ba wajen samun wutar lantarki mai ɗorewa, sannan mu ba matasa dama su zama masu dogaro da kai ta hanyar sana’a.”
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban gidauniyar, Alhaji Da’u Aliyu Abubakar, ya ce gidauniyar za ta ci gaba da tallafawa matasa da ilimi, kayan aiki da jari, domin rage zaman banza da bunkasa fasaha a Arewacin Najeriya.
Matasan da suka amfana sun nuna godiyarsu, inda suka ce wannan tallafi zai sauya musu rayuwa, tare da bai wa al’ummarsu hasken ci gaba ta fannin wutar lantarki.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News15 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
