Connect with us

News

‎Yan Bindiga Sun Sace Daraktoci 6 Na Ma’aikatar Tsaro Ta Kasa

Published

on

AFGHANISTAN UNREST TALIBAN

Fargaba ta mamaye ma’aikatan gwamnatin tarayya bayan da yan bindiga suka sace daraktoci shida na Ma’aikatar Tsaron Ƙasa a kan hanyar Kabba–Lokoja.

‎Rahotanni sun ce an sace su ne a ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025, yayin da manyan jami’an ke tafiya daga Legas zuwa Abuja domin jarabawar karin girma.

Advertisement

Kotu Ta Umarci A Kamo Soja Kan Zargin Kisan Jami’in KAROTA A Kano

‎Majiyoyi sun shaida wa Jaridar vanguard cewa maharan sun yi kwanton-bauna tare da tare ayarin motocin jami’an, inda suka yi awon gaba da su zuwa wani wuri da har yanzu ba a gano ba.

‎Kungiyar Association of Senior Civil Servants of Nigeria (ASCSN) a wata sanarwa da shugabanta, Shehu Mohammed, da Sakatare Janar Joshua Apebo suka fitar, ta bayyana sunayen daraktocin da aka sace kamar haka:

Advertisement

‎Mrs Ngozi Ibeziakor

Advertisement

‎Mrs C.A. Emeribe

Advertisement

‎Mrs C. Helen Ezeakor

Advertisement

‎Mrs C.A. Ladoye

Advertisement

‎Mrs J.A. Onwuzurike

Advertisement

‎Mrs Catherine O. Essien

Advertisement

Advertisement

‎Sanarwar ta kara da cewa, dukkansu ma’aikatan Command Day Secondary School (CDSS) Ojo, Lagos ne, kuma mambobin kungiyar kwadago.

‎Harin ya sake nuna karuwar matsalar garkuwa da mutane a kan manyan titunan Najeriya, lamarin da ke ci gaba da zama barazana ga jami’an gwamnati da sauran matafiya.

Advertisement

‎PLATINUM NEWS POST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending